Taron WACMaC 2023 An wallafa: September 20, 2023
SANARWAR MANEMA LABARAI
20 ga Satumba, 2023
Taron Kasuwar Babban Jari na Yammacin Afirka na 3 da ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu (WACMaC) 2023, za a gudanar da shi ƙarƙashin jagorancin Securities and Exchange Commission (SEC) ta Najeriya, da Securities and Exchange Commission ta Ghana, da AMFAO, tare da haɗin gwiwar West Africa Securities Regulators Association (WASRA), Economic Community of West African States (ECOWAS), West Africa Capital Market Integration Council (WACMIC), da West African Monetary Institute (WAMI).
Taron zai haɗa fitattun ƙwararru, masu kula da ƙa'idoji, masu tsara manufofi, da shugabannin masana'antu waɗanda za su raba iliminsu, gogewarsu, da dabarunsu domin gabatar da hanyoyin magance ƙarancin ababen more rayuwa a yankin. WACMaC 2023 yana ba da wata dama ta musamman don yin tattaunawa mai ma'ana, musayar fahimta, da ƙulla haɗin gwiwa da zai taimaka wajen tsara makomar kasuwannin babban jari. Wannan ƙarancin ababen more rayuwa babban ƙalubale ne ga ɗorewar ci gaban yankin. Saboda haka, domin cike wannan giɓi, ana ƙara buƙatar amfani da sabbin hanyoyin samar da kuɗi da zaɓuɓɓukan samar da kuɗi masu ɗorewa don tara kuɗaɗen da ake nema domin biyan muhimman buƙatun ababen more rayuwa na yankin, bunƙasa tattalin arziƙi, da cim ma manufofin ci gaba mai ɗorewa.
Taron bana yana da muhimmanci na musamman, domin masu ruwa da tsaki sama da 300 za su hallara a birnin Legas, a Eko Hotels and Suites Lagos, daga 25- 26 ga Oktoba, 2023, don tattauna babban jigon nan: ‘Ƙarancin ababen more rayuwa da samar da kuɗi mai ɗorewa a haɗaɗɗiyar Kasuwar Babban Jari ta Yammacin Afirka’.
Haka kuma, a lura cewa halartar taron ta takaita ga waɗanda aka gayyata kawai; za a ba da izinin shiga ne bayan yin rajista da nuna katin shiga a wurin taron.
Sa hannu
Lamido Yuguda
Babban Darakta, SEC kuma Shugaban WASRA