Gargadi kan Mai Gudanar da Harka Ba Bisa Doka Ba – My Shares da UYJ Multitrade Limited An wallafa: March 6, 2025
GARGADI KAN MAI GUDANAR DA HARKA BA BISA DOKA BA!
My Shares da UYJ Multitrade Limited
An jawo hankalin Securities and Exchange Commission (SEC) ga ayyukan MY SHARE mai aiki ƙarƙashin sunan UYJ MULTITRADE LIMITED, wanda ke gabatar da kansa a matsayin Mai Ba da Shawarar Zuba Jari/Manajan Asusun Zuba Jari a Kasuwar Jari ta Najeriya
Hukumar tana sanar da masu zuba jari cewa MY SHARE da UYJ MULTITRADE LIMITED BA SU DA RAJISTA don gudanar da kowane irin aiki a Kasuwar Jari ta Najeriya.
Saboda haka, ana shawartar jama’a su guji yin mu’amala da MY SHARE da UYJ MULTITRADE LIMITED ko wani wakilinsu game da kowace harka/ma’amala da ta shafi zuba jari a kasuwar jari ta Najeriya.
Hukumar tana amfani da wannan dama don sake jaddada cewa yin mu’amala a Kasuwar Jari ta Najeriya da ƙungiyoyin da ba su da rajista kuma ba sa ƙarƙashin kulawar ƙa’idoji yana jefa masu zuba jari cikin haɗarin damfara da yiwuwar asarar jari. Saboda haka, ana tunatar da masu zuba jari su tabbatar da matsayin kamfanoni da ƙungiyoyin da ke bayar da damar zuba jari a tashar Hukumar da aka ware – www.sec.gov.ng/cmos, kafin su yi mu’amala da su.
SA HANNU
HUKUMAR GUDANARWA