Yadda Lamunin Sayen Hannun Jari da Jinginar Jari ke Aiki An wallafa: November 13, 2023

Wannan kuɗi ne da aka karɓo a matsayin lamuni daga cibiyar kuɗi domin sayen hannayen jari, tare da jinginar jarin da aka riga aka yi. Lamunin sayen hannun jari da jinginar jari, wanda kuma ake kira ƙara ƙarfin jari ta hanyar karɓar bashi, na iya ƙara ribar zuba jari. Haka kuma yana iya ninka asara.

Yadda Yake Aiki

Idan mai zuba jari ya karɓi lamuni domin sayen hannayen jari, yawanci ana ajiye hannayen jarin da aka saya da lamunin a hannun mai ba da lamunin a matsayin jingina. Idan aka gaza biyan lamunin, ana iya sayar da hannayen jarin domin biyan bashin.

Fa'idodi

  • Zai iya kawo riba mai yawa
  • Yana ba masu zuba jari damar cin moriyar damammakin kasuwa.
  • Yana ƙara ƙarfin mai zuba jari wajen faɗaɗa kundin jarinsa.
  • Yana ba da damar samun ƙarin kuɗi cikin sauri. Mai zuba jari ba sai ya sayar da jarin da yake da shi ba domin haɗa basussuka wuri ɗaya ko yin wasu sayayya.

Illoli

  • Zai iya zama hanya mai haɗari sosai
  • Yana iya haifar da asarar jarin da aka yi amfani da shi a matsayin jingina idan aka gaza biyan lamunin
  • Yana iya haifar da asarar kuɗi idan darajar hannayen jari ta ragu
  1. Koma Babban Shafi
  2. /
  3. Aikin da Aka Ɗora Mana
  4. /
  5. Ci gaba
  6. /
  7. Ilimin Masu zuba jari
  8. /
  9. Ka'idojin zuba jari
  10. /
  11. Yadda Lamunin Sayen Hannun Jari da Jinginar Jari ke Aiki